
DAGA DANDALIN IS’HAQ IDRIS GUIƁI
Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, 22 ga watan Jumada Sani, shekarar 1444 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da 15 ga watan Janairu, shekarar 2023.
1. Ƙasar Spain ta ce za ta taimaka wa Nijeriya, a ƙoƙarin da Nijeriyar take yi wajen magance abubuwan da suka haifar mata da ta’addanci.
2. Gobe Litinin idan Allah Ya kai mu, Kwankwaso, da Peter Obi da Mahmood Yakubu na hukumar zaɓe, za su kasance a Chatham House na Ingila domin yin batu a kan zaɓukan da suke ci gaba da ƙaratowa. Sai kuma Atiku da ya ɗau alƙawarin gyara masana’antar mulmula ƙarafa ta Ajakuta.
3. Duk da gargaɗin da Babban Bankin Nijeriya ya yi wa bankuna, cewa bai so daga Juma’ar da ta gabata, ya sake jin sun ba jama’a tsofaffin kuɗi, ai kuwa har zuwa asubahin nan, tsofaffin kuɗin suke bayarwa ba sababbi ba.
4. Soludo gwamnan jihar Anambara, ya roƙi shugaban ƙasa Buhari ya sako masa Kanu. Soludon ya ce shi zai tsaya masa.
5. Shalkwatar ‘yan sanda da take Kano ta yi gobara.
6. An sake ceto mutum biyu, daga cikin waɗanda aka sace a tashar jiragen ƙasa da ke Edo.
7. A watan jibi, za a soma haƙo man da aka gano a jihar Nasarawa.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Ga ɗaya daga cikin waiwayen da na kalato muku, na sa a rubutuna na shekaranjiya kamar haka:
‘Daga Abduljalil Ismail Ajis
Yanda Kalmar “Ɗan Iska” Ta Samo Asali A Matsayin Zagi a Harshen Hausa
Tabbas a Hausa irin ta dauri, “ɗan iska” ba a kallonsa a matsayin mutumin banza. Ma’anar kalmar ta sauya ne bayan zuwan addinin Musulinci, kuma ma’anar ta ƙara muni ne musamman bayan jihadin Shehu Mujaddadi Usmanu a farkon Ƙarni Na 19!
Amma kafin shaharar Musulinci a ƙasar Hausa, kalmar “ɗan iska” ba zagi ba ce ba ko cin mutunci. Ba ta da bambanci da “ɗan koli”, ko “ɗan dako”, ko “ɗan doka”, ko “ɗan janhol”, ko kuma “ɗan kamasho” a ma’anar bayyana sana’a ko rukunin wasu mutane a cikin al’umma!
“Iska” na da ma’ana biyu a harshen Hausa:
1. Iska: Tana da ma’anar “Air” ko “gas” a Ingilishi, ko kuma “reah” a Larabce. Wato dai iska mai kaɗawa, wadda ke sanyaya abu ko gari.
2. Isaka: Tana da ma’anar “jinn” ko “spirit” a Ingilishi, da kuma “jinnu” a Larabce. Jam’in iska a wannan ma’anar shi ne “iskoki” ko “iskokai”.
Kamata ya yi mu fara fahimtar ma’anar kalmar “ɗan iska” da kuma “iska” a matsayin zagi.
To asali “ɗan iska” na nufin “ɗan bori”, wato mai hawa iska, ko ince wanda aljanu ke zuwa su shiga jikinsa sakamakon gayyato su da aka yi a yayin kiɗan garaya ko kiɗan bori.
To a bisa al’ada, sai ya zamana duk masu bori ko mu’amulla da inda a ke yinsa ba su da tarbiyya irin ta Islama, musamman a fannin aikata masha’a, da fidda tsiraici ko kalaman batsa.
Wannan dalili ne yasa a hankali ma’anar ta sauya da ga bayyana wasu mutane masu yin wata sana’a ko al’ada (bori), ta koma zagi. Domin duk wanda a ka bayyana da waccan ɗabi’a to ana kallonsa a matsayin “wayward” (tambaɗaɗɗe)!’
Is’haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.