
Samari ku daina bata lokacinku wajen neman aurena ni sai mai mata- mawakiya Haibat
Fitacciyar mawakiya kuma jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Habiba Hassan da ake yi wa lakabi da Haibat ta ce yaudarar da samari suka yi mata ya sa ta yanke kauna da auren saurayi, ta ce yanzu ita burinta shi ne ta aure mai aure.
Haibat ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da tsahar radio Dala da ke jihar Kano.
Ta ce ba za ta iya manta tsan-tsar yaudarar da samari suka yi mata ba a rayuwarta, shi ya sa ta yanke wannan hukunci.
Masha Allah