
DAGA DANDALIN IS’HAQ IDRIS GUIƁI
Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da huɗu ga watan Jumada Sani, shekarar 1444 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Janairu, shekarar 2023.
1. Tuni Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa ƙasar Mauritaniya.
2. Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce babu gaskiya a labarin da aka yaɗa cewa ta kai samame ofishin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Emefiele.
3. Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Emefiele, ya kammala hutunsa na shekara-shekara ya koma aiki gadan-gadan.
4. Bankuna sun ci gaba da ba jama’a tsofaffin kuɗi, wasu ma yagaggu suna warin bola.
5. :Yan siyasa suna ci gaba da yaƙin neman zaɓe.
6. Mutane masu zuwa karɓar katin su na zaɓe a makarantar firamare ta Unguwar Mu’azu Kaduna, sun yi ƙorafin idan sun je suna tarar da babu katin na su.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Na lura yawancin ma’aikatan rediyo da na sayar musu da littafin da na rubuta a kan Hausa a gidajen rediyo da talabijin da intanet, sun sayi littafin ne sun ajiye ba su karanta shi ba. Tunanin haka za ta faru na rubuta littafin shafukan ‘yan kaɗan ba yawa. Na lura da hakan ne saboda na saurari shirye-shirye kusan guda goma na waɗanda suka sayi littafin, kuma ban ji canjin da nake sa ran ji a Hausar tasu ba. Suna kammala shirin sai in ɗaga waya in kira su. In ce musu ‘wane da ji ba ka karanta littafina ba, ko ba ki karanta littafin ba’. Sai su ce ya aka yi na sani? Sai in ce musu abubuwan da na ankarar da su a kai, na ji ba a kiyayewa. Sai su ce gaskiya ne wallahi ba su karanta ba.
A ƙarshe ga wannan:
‘By: Halimatu Ahmad Kurfi
🚶MIJI NAGARI
—————————–
Most of the time a wajen wa’azozi ko lectures
ba a cika fadawa mutane halayen miji
nagariba sai dai ayita cewa halayen mace
tagari. Ga wasu daga cikin halayen miji
nagari:
1.Shine wanda yake ciyar da iyalinsa idan
shima yaci, yake shayar dasu idan shima
yasha.
2. Kuma yake tufatar dasu idan ya suturta
kansa.
3.Shine wanda zai zamo zaki a waje, damo
acikin gida. Ko kuma yazamto kamar air
condition wato, a waje yake zafi amman aciki
sanyi yake bayarwa.
4. Shine wanda ya hada wassu siffofi guda 10
wadanda Allah Ta’ala Ya ambacesu acikin
suratul Ahzab aya ta 35.
5. Miji nagari shine wanda yakeson matarsa
bayan aurensu fiye da yadda yaso ta a layi.
6. Shine mai kishin matarsa. Domin Sayyidil
waraa Sallallahu alaihi wasallam yace: “duk
wanda baya kishin matarsa bazai shiga
aljannah ba”.
7.Shine wanda ya dauki aure amatsayin
Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin
dadin rayuwa kawai.
8. Shine wanda ya dauki matarsa amatsayin
abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma
abokiyar shawararsa.
9.Shine wanda ba ya zagin matarsa, baya cin
mutuncinta, ba ya cin zalinta, baya ha’intarta
koda a bayan idonta ne.
9. Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin
amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba
cutarwa.
10. Shine wanda idan ya fahimci halayen
matarsa, yake hakurin zama da ita tare da
kyautatawa domin neman rahamar Allah
Ta’ala.
11. Shine wanda idan zai yi magana da
matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko
karya acikin ayyukansa da zancensa.
12. Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewar:
Iyayen matarsa, Iyayensa ne. ‘Yan uwanta ma
‘yan uwansa ne. Danginta ma danginsa ne.
13. Shine wanda yake daukar cewa farincikin
matarsa shine farincikinsa. Kuma Problem
dinta, shima nasa ne.
14. Shine yake kokarin kiyaye sirrin matarsa,
kuma yake kokarin Kare mata mutuncinta
koda awajen ‘yan uwansa ne, tare da hikima
da.fahimtarwa.
15. Shine wanda baya fifita matarsa akan ‘yan
uwansa, kuma baya tauye mata darajarta.
Yana ba ma kowanne gefe nasa hakkinsa
kamar yadda shariah ta tanadar.
16. Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da
hakuri acikin zuciyarsa domin ya rika kashe
wutar tashin hankali da bacin rai aduk lokacin
da hakan ta
faru tsakaninsa da matarsa.
17. Shine wanda a kullum yake kokarin
tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin
Islama ba rayuwa irinta yahudu da nasaraba.
18. Shine wanda yake zaune da matarsa
komai da’di komai wuya ba zai dena nuna
mata soyayya ba wai don tafara yankwanewa
ko kuma karfinta
yafara raguwa.
19. Shine wanda yake bawa matarsa
compliments a duk lokacin datayi kwalliya ko
kuma tayi girki komai rashin dadinshi.
20. Miji nagari baya raki, baya ihu don yaji
abinci yayi yaji ko gishiri yayi waya. Sai dai
yace: “uwargida abincinnan yayi dadi iyaka,
sai dai gishiri
yayi mana shisshigi aciki’
Is’haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.