
An hana Babba Kaita zagi a mumbarin siyasa
Wani babban jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ya shawarci Sanata Ahmad Babba Kaita kan yawan zagi da yake yi a mumbarin siyasa.
Ahmad Babba Kaita dai shi ne Sanata mai ci yanzu da ke wakiltar shiyyar Daura mazabar shugaba Buhari a jihar Katsina. Yanzu haka kuma shi ke takarar Sanata a shiyyar ta Daura a zaɓen watan gobe na Fabrairu mai zuwa.
An sha dai zargin cewa Sanata Ahmad Babba Kaita na yawan zagi a mumbarin yakin neman zaɓe, inda ake zargin cewa a wasu lokuttan ma har suna ya ke kamawa.
Babban jigon jam’iyyar ta PDP da bai aminta a ambaci sunansa ba, ya ce bai kyautu dan siyasa mai kima irin Ahmad Babba ba, a ce yana ashariya a bainar jama’a. Inda ya kara da cewa zagi na rage kima da mutunci a idon mutane.
DCL Hausa ta jiyo jigon Jam’iyyar PDP din na cewa dattakun Ahmad Babba ya wuce a jiyo shi yana zagi kuma jam’iyyar PDP, jam’iyya ce ta masu tarbiyya irin Ahmad Babba Kaita.
Zaiga munin abinda ya shiifka In sha Allah tunda dai shi Mulki na Allah ne ba zagi da cin mutuncin jama’a ba ke badashi ba, kaga wannan ta nuna cewar baida wata sauran kima da daraja a idanun mutanen kirki Kuma wannan ta nuna cewar irin sune ke Kai matasa ga zagin shugabanni da na gaba dasu ba tare da sanin illar hakan ba domin sunga manyan su nayi don haka wannan ta nuna Karara cewar bai dace da wakilcin da yake ba na majalisaar dattawa domin ba a san dattijo da rashin tarbiyya ba a aldance da addinan ce.
Don haka zabi ya rage ga mutane don su San irin mutanen da suke zaba wajen wakilcin su.