
Dikko Radda ya je neman kuri’a a yankunan da ayyukan ta’addanci suka yi kaurin-suna a Katsina
Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar APC Dikko Umar Radda ya bi ta yankunan da suka yi kaurin-suna wajen yawan ‘yan ta’adda a shiyyar Funtua domin yakin neman zaben.
A cikin wata sanarwa daga jami’in yada labaran kwamitin yakin neman zaɓen Dikko/Jobe, Malam Ahmad Abdulkadir ta ce dan takarar ya ratsa mazabun kananan hukumomin Sabuwa da Faskari a inda ake da daba-dabar ‘yan ta’adda domin samun sahihan bayanai da yadda zai bullo wa batun tsaro idan ya ci zaɓe.
DCL Hausa ta ba da labarin cewa ko a shiyyar Katsina, yankuna irin na kananan hukumomin Jibia, Batsari, Safana da Danmusa sai da dan takarar Gwamnan ya ratsa su ya je dukkanin mazabun lungu da sako domin jin ta bakin mutanen yankin game da hakin da suke ciki, da alkawurran da ya daukar musu.
Dikko Radda ya jajanta tare da tausaya wa wadannan al’ummomi, ya kuma ba su tabbacin cewa zai yi bakin kokarinsa domin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma idan aka zaɓe shi.
Sanarwar ta ce Dikko Radda ya ba da gudunmuwar babura ga ‘yan sintiri na garin Damari da ke karamar hukumar Sabuwa.