
DAGA DANDALIN IS’HAQ IDRIS GUIƁI
Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da bakwai ga watan Jumada Sani, shekarar 1444 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin ga watan Janairu, shekarar 2023.
Kamar kowacce Juma’a, an jima da safe sai a nemi jaridar Leadership Hausa don karanta shafina, ko a nemeta a dandalinta na intanet. Har ila yau a dandalin na intanet, za a iya leka jaridar Kainuwa, da ta AREWA Daily-Post, da Taskar Guiɓi da ke DCL Hausa da sauransu don duba rubutuna na yau da kullum. Sai kafofin watsa labaru irin su talabijin na Farin Wata da ke Abuja, da Talabijin na DITV da rediyon Alheri da ke Kaduna.
Yanzun ga kanun labarun
1. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya gana da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Emefiele a fadarsa da ke Abuja, inda suka sakaya ƙofa suka yi ƙus-ƙus-ƙus cikin sirri.
2. Majalisar Wakilai ta yunƙura, a kan samar da wata cibiya ta bincike a kan ƙaro wato Gum Arabic, domin bunƙasa fitar da shi ƙasashen waje.
3. Hukumar kula da lamuran masu shari’a, ta nuna rashin jin daɗinta, a game da ba a biyan masu shari’a da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu.
4. Bankunan kasuwanci suna ci gaba da ba jama’a tsofaffin kuɗi, shi kuma babban bankin Nijeriya yana ci gaba da musu barazanar hukunta su a kan abin da suke ci gaba da yi.
5. A Edo, bayan kammala ceto mutanen da aka yi fashinsu a tashar jiragen ƙasa ta Edo, an kama sarakuna biyu, da wasu mutum 5, da ake zargi da hannunsu.
6. A jihar Kwara, an yi fashin wasu direbobin manyan motoci su huɗu, ɓarayin nasu sun yi wa kowanne direba kuɗi, Naira Miliyan Biyar-Biyar ko kuɗi ko bari.
7. Gwamnatin jihar Barno, ta ba ‘yan makaranta hutun mako guda, domin waɗanda shekarunsu na jefa kuri’a suka kai, su je su karbi katinsu na zaɓe.
8. Gwamnatin jihar Legas ma ta ba da hutu na kwana huɗu, domin kowa ya je ya karɓi katinsa.
9. Gwamnatin Tarayya, ta ce za ta kashe kashi 60 cikin 100 na kuɗaɗen shiga da za ta samu a shekarar nan, wajen biyan bashi.
Mu yi Juma’a lafiya.
Af! Da asubahin nan ina shirin soma wannan rubutu, sai ga wannan saƙon:
Assalamun Alaika Malam idrees,Ina yimaka barka da dare,ya wunin gidanka da iyalanka duka? Yakuma kokarinka da jajircewanka? Allah ubangiji yaqara basira,baiwa,daukaka, karama,martaba,lafia da hasken ilimi amin.
Nace don Allah muma Muna baran shelantawarka. Amadadina ni Sameerah da mutanen yankina na gyallesu dake cikin birnin zaria. Muna roko ga gwabnati data yiwa Allah da girman Allah ta sanya Mana baki,hannu harma da kafafu su rokar Mana yan nepa su bamu wuta. Sai muyi kwana biyar shida nepa basu bamu wuta ba. Kuma idan mukai wadannan kwanakin idan suka tashi bamu sai dai subamu na second 3 zuwa second biyar. Shine iyakar wutar da zwmu sha sai Kuma wani bayan kwana uku zuwa kwana biyar din. Don girman ubangiji gwabnati ta tambayar Mana nepa shin Mai mutanen gyallesu sukai masu ne? Nagode sosai Allah ubangiji qara girma da daukaka Amin’
To Malama Samira wannan matsala taku ruwan dare ce a jihar Kaduna. Ta gagari kundila. Gara ma ku akan ƙyallaro muku. Shawarata a ci gaba da addu’a Allah Ya kawo mana shugabannin da za su tausaya mana, amma ba dai waɗanda suke kan mulki a yanzun ba. Waɗanda suke mulkinmu a yanzun a jihar Kaduna sunansu IHUNKA-BANZA.
Na yi nan
Is’haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.