
Babu tabbacin makusanta Buhari za su wanye lafiya bayan ya bar mulki- Fatuhu
Dan majalisar daga mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dansa na zumu Hon Fatuhu Muhammad ya ce ba shi da tabbacin cewa makusanta shugaban kasa Buhari za su wanye lafiya bayan kammala wa’adin mulkin shugaba Buhari.
Fatuhu ya bayyana haka a cikin wata hira ta musamman da gidan talabijin na TTV ta yi da shi da DCL Hausa ta bibiya.
Fatuhun ya ce “Buharin nan da ka fadi Buhari ne har gobe ba zai taba canzawa ba, zai gama mulkinsa lafiya zai kuma dawo gida lafiya, amma bani da tabbacin cewa duk na jikinsa zai zauna lafiya” Fatuhu Muhammad.