
Zan amince da sakamakon zabe, ko da ba ni na yi nasara ba- Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 ko da ba shi ya samu nasara ba.
Kwankwaso, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata ganawa da ya yi da daliban Jami’ar Abuja (UNIABUJA).
Dan takarar na NNPP, ya ce ya zama wajibi dole a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.