
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin CBN da yake jagoranta ba zai tsawaita wa’adin ranar 31.01.2023 na daina karbar tsofaffin takardun kudi ba.
Jaridar Daily Trust ta ce Emefiele ya fadi haka ne a wannan Talata bayan kammala wani babban taro na masu ruwa da tsaki da harkokin kudade a kasar nan. Gwamnan na CBN ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja cewa ba shi da labari mai dadi ga masu son a tsawaita wa’adin domin sun yanke shawarar ba za su kara wa’adin haramta amfani da tsofaffin kudaden ba.
Emefiele wanda dan majalisa Gudaji Kazaure ke zargi da hannu wajen badakalar kudade Naira Tiriliyan 89, ya yi amfani da wannan damar wajen musanta zargin shi da kansa. Ya ce a cikin shekaru bakwai Naira Biliyan 370 CBN ya tattaro daga harajin Stamp Duty ba kamar yadda ake zargin Naira Tiriliyan 89 ne aka tara ba.