
A karshe Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele ya yi magana a kan zargin da Gudaji Kazaure ya ke yi masa, ya ce kudaden ‘harajin stamp duty’ N370bn ne gwamnati ta tara a cikin shekaru bakwai, ba Tiriliyan 89 ba.
Emefiele, ya bayyana hakan a ranar Talatar nan a Abuja a taron kwamitin kula da harkokin kudi. Ya kuma jaddada cewa, Babban Bankin kasa CBN, ba ta boye Naira tiriliyan 89 ba da Gudaji ke cewa na an wawure.
A karshen shekarar da ta gabata ne dai dan majalisar wakilai mai wakiltar Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi na jihar Jigawa, Muhammed Kazaure, ya fito da wasu takardu na sakamakon binciken gwamnatin da ya jagoranta kan zargin satar kudaden harajin da ya kai naira tiriliyan 89 da Gudajin ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sany shi ya jagoranta.