
Jami’an tsaro mata sun koka kan rashin samari
A jihar Kaduna da ke Arewacin Nijeriya mata masu aikin kaki sun koka kan yadda samari ba sa zuwa neman aurensu.
Matasa da dama a jihar ta Kaduna sun bayyana wa Sashen Hausa na DW cewa yana da wahala ne su tunkari irin wadannan ‘yan mata masu sanye da kayan sarki sai dai idan ‘yan matan ne suka ba su kofar yin hakan.
Matashiya Maijidda Abdulkadir daya daga cikin jami’an tsaro mata daga jihar ta Kaduna ta sanarwa Dw Hausa cewa samari su rika fitar da tsoro da zarar sun gani suna so kawai su taya indai har suna son su.
Gaskiya zai yi wahala Inga mace jamia’ar tsaro in tunkareta da maaganar soyayyar,.