
Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero Kano ta musanta labarin cewa ta kara kudin makaranta ga dalibanta da kuma wadanda ke son shiga.
Gidan rediyon Premier da ke Kano ya ruwaito mai magana da yawun Jami’ar, Malam Lamara Garba, na cewa labarin ba gaskiya ba ne, don haka ya bukaci iyayen dalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulansu.
Garba ya ce har yanzu jami’ar ba ta samar da matsaya ba, kan kudin da ya kamata dalibai su biya a bana.
Tuni dai wasu jami’o’i musamman na Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da kara kudin makaranta ga dalibai, wanda hakan ke haifar da damuwa ga daliban da iyayensu.