
Koran Naja’atu aka yi daga APC
Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Asiwaju/Shettima, PCC, a ranar Talata ta ce an kori Naja’atu Mohammed, tsohuwar shugabar hukumar kula da kungiyoyin farar hula na yakin neman zaben Tinubu/Shettima, saboda rashin iya aiki da kuma fallasa muhimman bayanai.
Majiyar DCL Hausa ta Daily Nigerian ta ce Mahmud Jega, mai ba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Jega ya ce majalisar yakin neman zaben ta yanke hukuncin ne cikin gaggawa bayan gano yadda Naja’atu ke fallasa wasu muhimman bayanai ga jam’iyyun siyasa na adawa.