DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa

-

Shugaban jam’iyyar APC a Nijeriya Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar.
Wasu majiyoyi, sun tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa Abdullahi Adamu, wanda tsohon Gwamnan jihar Nasarawa ne ya aike da takardar ajiye mukamin nasa a fadar shugaban kasa, gabanin dawowar Shugaba Tinubu daga kasar Kenya.
Sanata Adamu da ya zamo shugaban jam’iyyar APC na kasa a Maris 2022 bayan zaben shugabannin jam’iyyar, ya aike da takardar ta ofishin shugaban ma’aikata ba fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamilla da yammacin Lahadi.
Wasu majiyoyi sun sanar da majiyar DCL Hausa cewa Sanata Abdullahi Adamu ya gaggauta yin murabus ne bayan da ya jiyo cewa akwai wasu gungun mutane da ke neman yi masa ature.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaban Nijeriya ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Mafi Shahara