DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An gurfanar da matar da ta caka wa wani mutum almakashi a Kano

-

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Gama ta jihar Kano ta tasa keyar wata mata mai suna Hafsa Musa a gidan gyaran hali bisa zarginta da daba wa wani mutum mai suna Buhari Mikail da almakashi.
‘yan sandan sun shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta aikata laifin ne a lokacin da fada ya barke tsakanin kawarta da mutumin inda ta daba wa masa almakashin ya kuma yi masa mummunan rauni.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba domin yanke mata hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jami’ar Kogi ta tabbatar da mutuwar malami a otel yayin da yake tare da wata ɗaliba

Rundunar 'yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar Olabode Abimbola Ibikunle, malami a sashen kula da harkokin Jama'a na Jami’ar Prince Abubakar Audu, Anyigba. Rahotanni...

Yadda ‘yan cabals ke turawa Buhari takardu a boye don ya sanya musu hannu – Tsohon shugaban ma’aikata, Gambari

Tsohon shugaban ma’aikata na Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana yadda wasu makusantan shugaban suka rika tsallake shi tare da mika takardu...

Mafi Shahara