DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun cafke ‘dilan’ wiwi cikin tashar mota a Kano

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Rayyanu Ibrahim, wanda aka fi sani da Yellow, a lokacin da yake siyar da tabar wiwi a cikin babbar tashar mota ta Mallam Kato da ke cikin kwaryar birnin jihar.
Rundunar ‘yan sanda ta Anti-Daba, karkashin jagorancin OC Musa Gwadabe, ta kama wanda ake zargin, bayan samun rahotannin sirri game da yadda yake gudanar da ayyukansa na cinikayyar tabar wiwi a cikin tashar motar ta Mallam Kato.
Da yake amsa laifin, Rayyanu Yellow, ya ce ya shafe sama da shekaru biyar yana sana’ar ta sayar da tabar wiwi.
Ya ce wannan shi ne karo na biyu da ‘yan sanda suka kama shi kuma a baya ya tuba amma daga bisani ya koma ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yadda ‘yan cabals ke turawa Buhari takardu a boye don ya sanya musu hannu – Tsohon shugaban ma’aikata, Gambari

Tsohon shugaban ma’aikata na Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana yadda wasu makusantan shugaban suka rika tsallake shi tare da mika takardu...

Ficewar Atiku daga PDP ya saba faruwa, muna sa ran zai dawo – Damagum

Shugaban riko na jam’iyyar PDP Ambasada Iliya Damagum, ya bayyana ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam’iyyar a matsayin wani lamari da ba...

Mafi Shahara