DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An yi yunkurin garkuwa da wani mutum, ‘yan sanda sun hana a Katsina

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa jami’anta sun yi nasarar dakile kokarin sata da garkuwa da wani mutum mai suna Tukur Adamu na kauyen Masaku cikin karamar hukumar Kankara ta jihar.
Mutumin mai shekara 40, kamar yadda sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ASP Aliyu Abubakar Sadiq ta ce hakan ta faru ne bayan samun kiran gaggawa da jami’anta suka yi, cewa masu garkuwa da mutane na yunkuri baje hajarsu a kauyen Masaku, amma cikin lokaci suka je suka dakile wannan yunkuri har suka ceto wannan mutumi ba tare da ya rasa ransa ba.
Sai dai sanarwar ta ce mutumin ya samu rauni ta dalilin harbin bindiga, amma dai an garzaya da shi asibiti, yanzu haka yana karbar magani.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba da irin kwazon jami’an da suka ceto mutumin, ya kara da cewa ‘yan sanda a jihar Katsina ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa...

Mafi Shahara