DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwace mulki daga hannun Abba gida-gida ka iya tayar da rikicin da zai mamaye Africa- NNPP

-

 Shugabancin jam’iyyar
NNPP ya yi gargadin cewa amfani da karfin iko wajen kwace nasarar da Abba Kabir
Yusuf ya samu a jihar Kano, ka iya tayar da hankali, wanda zai iya mamaye
Najeriya har ma ya tsallaka zuwa wasu kasashen Africa.

Google search engine

 

Ta cikin wata
sanarwa da mai rikon kwaryar shugabancin jam’iyyar Abba Kawu Ali ya sanyawa hannu
aka kuma rabawa Kungiyar kasashen yammacin Africa, da ofishin jakadancin
Kungiyar tarayyar turai da na kasar Amurka da Burtaniya, ta ce akwai manyan
alamu da ke nuna cewa jam’iyyar APC ta lashi takobin yin duk mai yiwuwa wajen
kawace mulkin duk da bata yi nasara ba.

Sanarwar ta ce idan
aka lura da yadda jihar Kano ke ciki, ana zaman dar-dar ne, saboda yadda jama’ar
da suka fita kwan su da kwarkwata suka zabi Abba, amma ake shirin kwace wa,
wanda matukar hakan ta tabbata shakka babu zasu iya tayar da rikici.

Sanarwar ta kuma kara
da cewa akwai hasashen cewa jama’ar Kano ba zasu yi hakuri irin wanda suka yi a
2019 ba lokacin da aka yi amfani da wasu dokoki wajen kwace mulki kiri-kiri.

Abba Kawu Ali, ya
kuma ce akwai bukatar wadannan hukumomi da kasashen duniya su sanya idanu kan
wannan shari’a su kuma tabbatar an yi gaskiya, matukar ba haka ba kuma akwai
yiwuwar jama’a su dauki doka a hannun su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaban Nijeriya ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Mafi Shahara