DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Adadin wadanda suka mutu a sanadin harin sojoji a Kaduna ya karu zuwa 120-Amnesty international

-

Google search engine

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty
International ta ce adadin wadanda harin bam din sojoji ya kashe a kauyen Tungar
biri na jihar Kaduna ya kai 120 zuwa yanzu.

Bayanai na nuna cewa har yanzu babu wani alamu a
aikace na daukar mataki kan sojojin da suka aikata wannan danyen aiki, in banda
Allah wadai da gwamnati ta yi.

Har ya zuwa yanzu dai akwai mutane fiye da 50 da ke
kwance rai a hannun Allah a asibiti suna karbar kulawar jami’an lafiya bayan
wannan abin takaici da ya rutsa da su.

Sai dai kuma adadin da Amnesty ta bayar ya ci karo
da wanda hukumar bayar da agaji ta kasa NEMA ta bayar wanda ke cewa kawo yanzu
mutane 85 ne suka mutu a sanadin harin, yayin da 66 suka jikkata.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an sojoji
ke hallaka mutane da sunan kuskure a arewacin Najeriya ba, inda kididdiga ke
nuna cewa ire-iren wadannan hare-hare sun kashe mutanen da basu ji ba basu gani
ba har sama da 400 daga 2014 zuwa yanzu, musamman a jihohin Borno da Zamfara.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Jami’ar Kogi ta tabbatar da mutuwar malami a otel yayin da yake tare da wata ɗaliba

Rundunar 'yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar Olabode Abimbola Ibikunle, malami a sashen kula da harkokin Jama'a na Jami’ar Prince Abubakar Audu, Anyigba. Rahotanni...

Mafi Shahara