DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ECOWAS ta dorawa sojojin kasashen Nijar, Mali, da Burkina Faso alhakin karuwar ta’addanci a yammacin Africa

-

Google search engine

Kungiyar kasashen yammacin
Africa ta ECOWAS ta zargi sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Nijar, Mali
da Burkina Faso a matsayin wadanda ke rura wutar ta’addanci a nahiyar


Shugaban majalisar
gudanarwar kungiyar Omar Tourey ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi
wajen bikin bude taron kungiyar kan tsaro da shiga tsakanin rikice-rikice karo
na 51 da aka fara a Abuja.

Tourey ya ce juyin mulkin
da sojojin suka yi, ya rusa duk wani tsari ko kokari da kungiyar ke yi na
tabbatar da tsaro a yankin.

Ya kuma kara da cewa jan
kafar da sojojin ke yi wajen mika mulki hannun farar hula na baiwa ‘yan ta’adda
da masu daukar nauyin su kara azama wajen kaddamar da hare-hare kan fararen
hula.


Tourey ya kuma nuna
takaicin sa kan yadda sojojin ke amfani da juyin mulkin wajen yada farfaganda
irin ta siyasa yayin da suke nunawa duniya cewa zaluntar su ake yi.


Kididdiga ta nuna cewa juyin mulkin da
sojoji suka yi a wadannan kasashe ya jefa jama’a kusan miliyan 5 cikin yunwa da
bakin talauci, sai wasu miliyan 2.5 da suka rasa muhallan su, inda ya tilasta
rufe makarantu fiye da dubu 9.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara