DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutanen kauyen Tudun Biri sun maka FG kotu, su na neman diyyar N33bn

-

Mutanen kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sun maka gwamnatin tarayya kotu tare da neman diyyar kudi Naira bilyan 33.
Matakin mutanen ya biyo bayan kashe mutane sama da 100 da jirgin sojan Nijeriya ya yi a makon jiya. Sai dai sojojin sun amsa laifin su, sun kuma ce hakan ta faru ne bisa kuskure.
Ibtila’in ya fada wa al’ummar yankin a lokacin da suke bikin Mauludi.
Tuni dai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci da a gudanar da bincike mai zurfi don gano hakikanin abin da ya faru. Sannan ya ma ja kunnen sojojin da sauran jami’an tsaro da kada su kuskura hakan ta sake faruwa a sassan kasar.
Alhaji Dalhatu Salihu ne ya shigar da karar a babbar kotun jihar Kaduna a madadin al’ummar kauyen Tudun Biri ta hannun lauyansu Mukhtar Usman.
Mutanen kauyen na kuma bukatar a ba su hakuri a rubuce a kuma buga a manyan jaridu uku na Nijeriya.
Har yanzu dai ba a kai ga saka ranar da za a fara sauraron karar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara