DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC na zawarcin Wike

-

Jam’iyyar APC ta ce tana nan tana zawarcin tsohon Gwamnan Rivers kuma ministan Abuja a halin yanzu Mr Nyesom Wike zuwa jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce muddin ya karbi tayinta na komawa, zai zama shi ne babban jigo kuma jagoranta a jihar Rivers.
Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa Wike na yawan nanata cewa shi dan jam’iyyar PDP ne duk kuwa tarnaki da ciwon kan da ake ganin ya ba PDP bayan ya fadi zaben fitar da gwani a zaben shekarar 2023 da Atiku Abubakar ya kayar da shi.
A baya-bayan nan, baraka ta kunno kai tsakanin Wike da yaronsa a siyasa Gwamnan Rivers na yanzu Sim Fubara da hakan ya jaza tsagewar majalisar dokokin jihar gida biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara