DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dan majalisa a Kano ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya

-

Dan majalisar wakilai da daga karamar hukumar Fagge a jihar Kano Mohammed Bello Shehu ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya a mazabar da yake wakilta.
Wannan yunkuri dai ya sa masu ruwa da tsaki na yankin Fagge da kewaye a jihar ta Kano suka sa kafa suka shure, su na ganin cewa kamar ba wannan al’umma ke bukata ba.
A al’adance dai, al’ummar Hausawa na yi wa ‘ya’yansu kaciya a zamanin sanyi.
Dan majalisar da yake a jam’iyyar NNPP ya bugi kirjin daukar nauyin yara sama da 1,000 da za a yi musu kaciya a mazabu 11 da yake wakilta.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa har ma an kaddamar da wannan aiki a ranar Asabar a cibiyar kiwon lafiya ta Ofishin Galadima da ke mazabar Fagge B.
Wannan lamari dai ya sa ana ta ce-ce-kuce har wasu na ganin kamar dan majalisar ba zai iya cika alkawarin da ya dauka ba a zamanin yakin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu...

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

Mafi Shahara