DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Lantarkin Nijeriya za ta kara inganta a shekarar 2024 – Minista

-

Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin ma’aikatarsa na ba da fifiko ga samar da wutar lantarki a kasar a cikin shekarar 2024.
Ya ce hakan ya yi dai-dai da tsarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na sauya wutar lantarki a sakonsa na sabuwar shekara.
Mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, Mista Bolaji Tunji, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja jiya Litinin.
Yace “Saboda fahimtar muhimmiyar rawar da wutar lantarki ke takawa wajen bunkasar tattalin arziki, watanni ukun farko da na hau ofis na mayar da hankali kan bincike, tuntubar masu ruwa da tsaki, da kuma tsara dabaru.
“Tare da ingantaccen tsarin aiwatarwa, yanzu lokaci ya yi da za a ɗauki kwakkwaran mataki.
“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shine haɓakawa da rarrabawa da kayan aikin watsawa don rage asarar da ake samu ta kasuwanci” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu...

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

Mafi Shahara