DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sadiya Umar Faruq za ta gurfanar a gaban EFCC

-

Tsohuwar minista jin kai a lokacin mulkin Shugaba Buhari Sadiya Umar-Farouq za ta gurfana a gaban jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan 37.
A makon jiya ne dai EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar domin ta amsa tuhume-tuhume da ake yi mata lokacin da ta ke rike da mukami.
Ana tuhumar ta kan zurarewar wasu kudade kimamin N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar da su a yayin da ta ke jagorancin ma’aikatar ta jin kai.
Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun shaida wa wakilin majiyar DCLHausa ta Daily trust a ranar Talata cewa, an bukaci tsohuwar ministar ta bayyana a gaban masu bincike a hedikwatar hukumar ta EFCC da ke Jabi, Abuja, da karfe 10:00 na safiyar Larabar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu...

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

Mafi Shahara