DCL Hausa Radio
Kaitsaye

EFCC na neman iznin kamo tsohuwar ministar jin kai a gwamnatin Buhari, Sadiya Umar Faruq

-

Jami’an hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa tu’ammati EFCC na duba yiwuwar neman takardar iznin kamo tsohuwar ministar jin kai a gwamnatin Buhari, Sadiya Umar Faruq.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa hakan ya biyo bayan kin amsa goron gayyatar da hukumar ta yi mata a ranar Laraba.
Sadiya Umar Faruq dai da hukumar ta shirya karbar bakuncinta da misalin karfe 10 na safiyar Laraba, ana tuhumarta da batun wasu kudi da suka kai darajar sama da Naira bilyan 37.
Ana dai zargin cewa an wawure wadannan kudaden a zamanin da take minista ta hannun wani dan kwangila Mr James Okwete.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Jami’ar Kogi ta tabbatar da mutuwar malami a otel yayin da yake tare da wata ɗaliba

Rundunar 'yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar Olabode Abimbola Ibikunle, malami a sashen kula da harkokin Jama'a na Jami’ar Prince Abubakar Audu, Anyigba. Rahotanni...

Mafi Shahara