DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba zamu amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba-NLC

-

Google search engine

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta mayarwa da shugaban kasar martani kan
alkawarin sa na sabuwar shekara game da shirin yiwa ma’aikatan kasar karin albashi.

Kungiyar karkashin jagorancin Joe Ajero ta ce babu wani dalili da zai sa
ta amince gwamnatin tarayya ta yi gaban kanta wajen Karin albashi, a wannan
karo ya zama wajibi a tattauna da su kafin karin albashin.

Shekarar 2018 ce shekara
ta karshe da gwamnatin tarayya ta tattauna da kungiyar kwadago kafin kara albashi.

Kungiyar ta ce gwamnati ta
jima tana yi mata dadin baki game da karin albashi, sai dai a wannan karon ya
zama wajibi ta dauki mataki, don shiga yarjejeniya da gwamnatin tarayya a watan
Afrilu mai zuwa.

Sai dai babban abinda ya
fi daukar hankali a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar shine, yadda ta ce ba
zata amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Al’ummar Najeriya sun fada
cikin halin masti tun bayan da gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur da
yadda darajar naira ke kara sulalewa, yayin da kayan masarufi ke kara tsada
dalili kenan da ya sa kungiyar kwadagon ke ganin bai kamata ma’aikata su rika
karbar kasa da naira dubu 200 a matsayin albashi ba.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa...

Mafi Shahara