Birnin Lagos ya
zarta Dubai na hadaddiyar daular Larabawa da birnin Miami na Amurka kyau a
duniya.
Kamar yadda wata
mujalla da ke sanya idanu kan kyawun birane a duniya mai suna Time out ta wallafa,
ta ce birnin Lagos na Najeriya shine na 19 cikin jerin birane mafiya kyau a
duniya.
Biranen Lagos, da Cape town na Africa ta
Kudu da kuma Accra na Ghana su kadai ne suka shiga cikin jerin a kasashen
Africa.
Mujallar na amfani da ma’aunin dadin
abinci da arhar sa, al’adun gargajiya, ababen more rayuwa, yanayin tsaro, mu’amala,
guraren tarihi da sauran su wajen tantance burunkasar birni.