DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kalaman sanata Ndume ba komai ba ne illa yukurin tunzura ‘yan arewa-Fadar shugabab kasa

-

Gwamnatin tarayya ta mayar wa da sanata Ali Ndume martani
game da kalaman da yayi da ke nuni da cewa gwamnatin na kullawa ‘yan arewa wata
makarkashiya, shine ma dalilin da ya sa zata mayar da wasu sassan CBN da
hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos.

Google search engine

Ta cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce wannan
ba komai bane illa yunkurin tunzura ‘yan arewa a kan ‘yan kudu, kuma ba zai yi
nasara ba.

Kalaman na Sanata Ndume sun biyo bayan sanarwar
gwamnati na mayar da wasu sassa masu muhimmanci na babban bankin kasa CBN da
kuma hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos ba tare da
bayar da wani gamsashen dalili ba.

Tun bayan fitar wannan labari ne ‚yan arewa ke mayar
da mabanbantan martani, yayin da wasu ke ganin wannan ba komai bane illa
yunkurin mayar da arewa saniyar ware, inda kuma wasu ke da ra’ayin cewa hakan wani
salo ne na shirin raba kasar.

Baya
ga wannan an kuma zargi gwamnatin ta Tinubu da yunkurin mayar da fadar shugaban
kasa kachokan zuwa jihar Lagos, sai dai tuni gwamnatin ta musanta wannan zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa...

Mafi Shahara