DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sanusi Lamido ya goyi bayan mayar da wasu sassan CBN zuwa Lagos

-

 

Google search engine

Tsohon
gwamnan babban bankin Najeriya kuma sarkin Kano na 14 Sanusi Lamido Sanusi ya
goyi bayan gwamnatin tarayya a shirin da take yi na mayar da wasu sassan babban
bankin CBN kasar zuwa birnin Lagos.

 

Yayin da
yake mayar da martani kan masu sukar tsarin, Sanusi ya ce abinda suke yi abu ne
mai matukar hadari ga makomar bankin, don haka gatan da za’a yi masa kadai
shine mayar da shi jihar Lagos.

 

Sarki Sunusi mai murabus ya kuma ci gaba da cewa masu
wannan suka musamman ma’aikatan bankin ba kowa bane illa karnukan farautar ‘yan
siyasa masu samun kudade da babban bankin, don haka akwai bukatar su yi
gaggawar daina sukar gwamnati.

Ya ce mayar da sassan bankin zuwa Lagos zai saukaka
aiki, da kuma rage kashe kudaden gudanarwa da ake yi kowacce rana.

Sai dai
ya ce akwai bukatar sassa irin su, fannin tsara dubarun tattalin arziki, ofishin
mai binciken kudi, da ofishin takaita asara da sauran sassa da ke aiki kai
tsaye da ofishin gwamnan bankin su ci gaba da zama a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara