Gwamnatin jahar Kebbi ta rufe wasu man’yan makarantu biyu masu zaman kansu bisa rashin biyan haraji har na tsawon shekaru biyu.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin Kwamishinan ilimin na jahar Isa Abubakar Tunga ta nuna cewa gwamnati bazata yi musu da wasa ba saboda sakaci da suka yi bayan tunatar da su da kuma kashedi da gwamnati ta yi garesu a lokuta daban-daban.
Makarantun da aka rufe sune Kwalejin ilimi da kimiyyar kiwon lafiya ta LamiÉ—o Umaru Mutube da ke ĆŠakin- Gari da Kwalejin Kimiyya da fasahar kiwon lafiya ta SAHAM da ke Zuru.
Gwamnatin ta Kebbi ta ce babu wata bita da Ć™ulli a batun dakatarwa kuma da zĂŁrar sun biya kuÉ—aÉ—en da gwamnati ke bin su za’a buÉ—e makarantun su ci gaba da harkokin karantarwa.
Binciken hukumar kula da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO na 2012 ya nuna cewa Jihar Kebbi dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke baya a ɓangaren ilimi bayan jihohin Katsina, Taraba, Borno da Jigawa.