DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Najeriya ta sanya Interpol cikin masu bincike kan kwaikwayar sa hannun shugaba Buhari

-

 


Google search engine

Gwamnatin Najeriya
ta bukaci ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol su sanya wasu mutane uku cikin
jerin wadanda suke nema ruwa a jallo sakamakon zargin su da hada baki wajen
kwaiwakayar sa hannun tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda suka fitar
da dala miliyan 6 da dubu dari 230 daga asusun kasar.


Mutanen da ake zargi sun hadar
da Adamu Abubakar da Imam Abubakar da kuma Odoh Eric Ocheme.

Tuni dai gwamnatin kasar ta shigar da
karar mutanen uku, kan zargin satar bayanan tsohon shugaban kasa, yiwa kasa
zagon kasa da yaudarar ma’aikatan gwamnati.

Tun farko mutanen sun rubuta
takarardar bayar da umarnin fitar da wadannan kudi daga asusun gwamnati dauke
da sa hannun shugaba Buhari, sannan suka kaiwa sakataren gwamnati na wancan
lokaci Boss Mustapha wanda ya fitar da kudin, karkashin babban bankin kasar.

Bayanai sun ce an yi
amfani da kudaden ne wajen raba su ga kungiyoyin da ke sanya idanu kan zaben da
aka gudanar a kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa...

Mafi Shahara