DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun gaji da ba talakawa hakuri, don suna gab da yi wa gwamnati tawaye – Sarkin Musulmi

-

Google search engine

Mai Alfarma
Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya gargadi gwamnatin Najeriya ta
gaggauta daukar matakin saukaka wa talakawa rayuwa da fatattakar yunwa, matukar
ba haka ba kuma ta kuka da kanta kan matakin da talakawan zasu dauka akanta.

Da ya ke yiwa manema
labarai jawabi a Arewa House da ke jihar Kaduna Sarkin musulmin yace sarakunan
gargajiya dana shugabannin addini sun gaji da tausar talakawa da kuma basu
hakuri, don haka babu makawa illa gwamnati dauki matakin saukaka rayuwa.

Ya ce a yanzu
talakawa sun kai geji kuma tura ta kai bango kana sarakunan gargajiya ba zasu
iya tare talakawa ba  idan suka fusata da
gwamnati.

Ya ce kullum maganar kenan da
gwamnati ke yi musu kan suci gaba da tausar talakawa, har zuwa yaushe ne za’a
ci gaba da bada hakuri? Har zuwa yaushe ne talakawa zasu ci gaba da mutuwa da
yunwa da sunan hakuri? a yanzu lokaci ne da gwamnati zata yi hakuri ta dauki
matakin da ya dace.

“Mun jima muna rokon talakawa, a
yanzu mun gaji, kunyar su muke ji, sun fara daina yarda da maganar mu, don babu
wata alamar sauki daga gwamnati don haka matukar gwamnati bata dawo cikin
hayyacin ta ba, to duk matakin da talakawa suka dauka tabbas ta kuka da kanta”
inji sarki musulmi.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara