DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Karin bayani kan takunkumin da ECOWAS ta janye wa Nijar

-

 

Kola Sulaimon / AFP

Google search engine

ECOWAS da shugabanninta sun lashe amansu bayan da a taron kungiyar
a Abuja, ta janye wasu daga cikin takunkuman da ita da kanta ta lafta wa Nijar
don ladabtar da sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimukuradiyya a shekrar
da ta gabata. A sanarwar da ECOWAS din ta fitar ta ce a hankali za ta janye
sauran, amma ta ce ta janye wa kasashen Mali da Guinea takunkuman kudi da
tattalin arziki. Sai dai ‘yan Nijar sun fi damuwa da bukatar a janye musu
takunkuman iyakoki da kudade da na wutar lantarki wanda kawo yanzu sanarwar ta
ECOWAS ba ta ce komai a kai ba. 




 

Tun bayan lafta wannan takunkumi dai, hukumomin mulkin sojan kasar
suka dukufa wajen lalubu hanyoyin rage radadin takunkumin amma kusan ba su yi
wani tasiri ba duba da yadda farashin kayayyakin musamman abinci ya ki sauka
tare da ci gaba da fuskantar matsalar rashin wadatuwar kudade a hannun mutane.

 

To sai dai duk da wannan yanayi da aka shiga sojojin suka ci gaba
da kafewa kai da fata ak an matsayin su har ma a karshe suka ayyana ficewarsu
tare da takwarorinsu na Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar baki
daya  don haka ne ga masu fashin baki irinsu Dr Gambo Alhaji Sani masanin
kimiyar siyasa a Jami’ar André Salifou ta Damagaram ke ganin dole ne kungiyar
ta ECOWAS ta rungumi kaddara domin kuwa ta ga ba wurin zuwa ne sai gona shi ya
sa ta ci tuwon fashin, mai sharhin ya shaida wa DCL Hausa cewa duk da ECOWAS ta
janye takunkuman amma zai wahala idan yanzu sojojin na Nijar za su janye fita
daga kungiyar da suka yi domin sun yanka sun ga jinni

Tun farkon wannan mako mai karewa ne dai rahotanni cire takunkumin
na ECOWAS kan Nijar ke yawo kafin a tsakiyar makon tsohon shugaban kasar
Tarayyar Najeriya Yakubu Gowon wanda ke cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS
ya yi kira ga kungiyar  da ta gaggauta cire Nijar din takunkumin da ta
kakaba mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Mafi Shahara