DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Har ‘yan adawa na yabon Gwamna Dikko wajen kokarin inganta tsaron jihar Katsina – Bala Abu Musawa

-

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya ce irin kwazon da Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ke yi wajen inganta tsaro ya sa har ‘yan adawa na yabonsa.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana a karamar hukumar Jibia, a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman da ke duba ayyukan da aka gudanar a kananan hukumomi 34 na jihar tare da ganawa da shugabannin jam’iyyar a matakin karamar hukuma da mazabu.
Ya ce Allah Ya hore wa Malam Dikko Umaru Radda fasaha da basirar da ya ke amfani da ita wajen ganin zaman lafiya ya inganta a lungu da sako na jihar.
Bala Abu Musawa ya buga misali da kafa matasan sa kai na ‘Community Watch Corp’da Gwamnan ya kaddamar suke ci gaba da ayyukan samar da tsaro tare da sauran jami’an tsaro a wuraren da ke fama da batun tsaron, inda ya ce wannan tunani ne mai kyau da ke haihuwar da mai ido a halin da ake ciki.
Mataimakin shugaban jam’iyyar wanda shi ne Ci Garin Musawa, ya kuma yaba da abin da ya kira kokarin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na bullo da alawus-alawus ga jagororin jam’iyyar APC tun daga matakin jiha har zuwa matakin mazaba, inda ya ce ya zuwa yanzu an biya alawus-alawus na cikon watanni uku, kuma za a ci gaba da yin haka don karfafa musu guiwar tafiyar da lamurran jam’iyya yadda ya kamata.
Ya kuma yi bayanin cewa ziyarar na da kuma nufin motsa harkokin jam’iyyar APC ganin cewa hukumar zabe ta jiha, ta sanar da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a shekara mai kamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara