DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Katsina za ta karbi bakuncin taron inganta tsaro da zaman lafiya na shiyyar arewa maso yamma

-

Gwnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da hadin guiwa tsakanin gwamnatin jihar da shirin bunkasa kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP su karbi bakuncin taron inganta tsaro da samar da zaman lafiya a shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya a jihar Katsina.
Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barr Abdullahi Garba Faskari ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da kwamitin tsare-tsaren yadda za a karbi bakuncin a madadin Gwamnan.
Taken taron shi ne dabarun inganta tsaro da zaman lafiya: shawo kan matsalolin ayyukan ta’addanci da sauyin yanayi.
Kwamitin na kunshe da mambobi 14 da Sakataren Gwamnatin jihar ne shugaba, sannan akwai shugaban ma’aikatan jihar Katsina da kwamishinonin yada labarai da na tsaro da lamurran cikin gida da kuma na shari’a.
A cikin wata sanarwa daga daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Yar’adua, ta ce daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai hada hannu da shirin UNDP da sauran hukumomin da suka dace don karbar bakuncin taron yadda ya dace a Katsina.
Kazalika, kwamitin zai shiga ya fita don ganin an saukaka zirga-zirga ga bakin da za su halarci taron, samar da wurin da Taron zai gudana, gayyatar baki da sauran abubuwan da suka shafi wannan taro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa...

Mafi Shahara