An dakatar da Maryam Mai Rusau daga jam’iyyar APC bayan hirarta da DCL Hausa
Maryam Mai Rusau dai ita ce shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
A cikin hirarta da DCL Hausa, Maryam Sulaiman ta soki lamirin gwamnatin Sanata Uba Sani, bayan aka jiyo Gwamnan na cewa ya gaji tarin basuka daga hannun Malam Nasir El-Rufa’i. Basukan da suka jaza har ba su iya biyan albashi a halin da ake ciki.
Ai da uba sanin aka hada aka ciwo bashin kuma Meye na complain yanxu