DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi yunkurin kai harin ramuwar-gayya a Danmusa jihar Katsina

-

Wani rahoto da DCL Hausa ta samu na cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba sun yi yunkurin shiga garin Danmusa, hedikwatar karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina cikin daren nan na Litinin.
Sai dai bayanai sun ce jami’an sun yi nasarar dakile wannan yunkuri hari da aka kira na ramuwar gayya. Yunkurin ‘yan bindigar ya biyo bayan wani aikin fatattakar ‘yan bindiga da jami’an tsaro aka sanar cewa sun yi a kauyen Katsira, inda bayanai suka ce jamian tsaro sun yi nasarar konawa tare da lalata mafakar ‘yam bindigar da dama.
Duk da dai a yayin samamen jami’an tsaron ba a ba da rahoton an kashe ko jikkata wasu ‘yan bindigar ba, amma wata majiya daga jami’an tsaro da ta nemi da kada a ambace ta, ta tabbatar da cewa an yi wa ‘yan bindigar barna mai yawa.
Hakan ne ma, kamar yadda majiyar ta sanar da DCL Hausa ya sa ‘yan bindigar suka yi zuga, da zummar ramuwar gayya a garin na Danmusa. Amma jami’an tsaro suka sake samun nasarar fatattakarsu.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, mutanen garin na Danmusa dai sun firgita, da hakan ya sa har wasu suka fara tunanin ko ma ‘yan bindigar sun shiga garin, a lokacin da suka ji karar harbe-harben bindiga a bayan gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Mafi Shahara