DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hisbah ta kama ɗan jarida a Katsina

-

Google search engine

Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta kama ɗan jarida Jamilu Mabai, wakilin gidan talabijin na Trust Tv a jihar Katsina.

Rahotannin da DCL Hausa ta samu sun nuna cewa hukumar ta Hisbah ta nemi dan jaridar ruwa a jallo sakamakon wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa ta Facebook, wanda yake da alaƙa da zargin cin mutuncin hukumar da shugabanta

An kama Mabai ne a wannan Talata bayan da ya je hukumar da niyyar haɗa rahoto na zargin da ake ma hukumar na harbe wani dattijo mai sana’ar faci da bindiga, wanda hakan ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara