DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaron Nijar sun cafke kasurgumin dan bindiga Baleri da hukumomin Nijeriya ke nema

-

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun sanar cewa sun yi nasarar kama kasurgumin dan ta’addar nan mai suna Baleri da hukumomin Nijeriya suka sanar cewa su na nemansa ruwa jallo.
Jami’an tsaro na rundunar nan ta musamman masu lakabin ‘farautar bushiya’ ne dai dake aikin kawo tsaro a jihar Maradi suka yi nasarar kama wannan dan bindiga dan asalin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Dan bindigar da ke gudanar da ayyukan sa a tsakanin kasashen na Nijar da Najeriya sojojin sun ce sun yi nasarar cabke shi ne a karamar hukumar Guidan Roumdji ta jihar Maradi a lokacin da yake tsaka da tsare-tsaren yadda za su kai hare-hare a kasashen biyu da yaran sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu...

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

Mafi Shahara