DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An sace lakcarorin jami’ar FUDMA jihar Katsina

-

Wasu bayanai da DCL Hausa ta samu daga jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma jihar Katsina, na cewa ‘yan bindiga sun sace tare da garkuwa da lakcarorin jami’ar guda biyu.
Bayanan sun ce ‘yan bindigar sun sace Prof Richard Kyaram da dansa mai suna Solomon a gidan da suke zaune a Unguwar GRA cikin garin Dutsinma, jihar Katsina.
Bugu da kari, ‘yan bindigar sun kuma sace karin wani malamin jami’ar da aka bayyana sunansa da Dr. Hamza duk a cikin Unguwar ta GRA, Dutsinma.
Lamarin kamar yadda DCL Hausa ta samu labari, ya faru ne da sanyin safiyar Litinin da misalin karfe 1am. Bayanai sun ce ‘yan bindigar da dauke da muggan makamai sun shiga Unguwar ta GRA suna harbin kan mai uwa da wabi, su na bi gida-gida kamar yadda majiyar DCL Hausa ta shaida mata.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin babu sahihin bayanin sashe wato ‘department da wadannan lakcarori suke a jami’ar ta FUDMA. Sannan babu cikakken bayanin ko wadanda suka sace su sun kira don neman kudin fansa ko a’a. Hakan ta faru ne ta dalilin rashin samun bayani daga sashen hulda da jama’a na jami’ar, bayan da aka buga wayar jami’in hulda da jama’a na jami’ar Malam Habib Umar Aminu, ba ya kusa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ma ba ya kusa da wayarsa a lokacin da DCL Hausa ta tuntube shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu...

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa. Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai,...

Mafi Shahara