DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 30 a wani sabon hari a kauyen Katsina

-

‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Kunamawa na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina a ranar Laraba.
Harin kamar yadda majiyar DCL Hausa ta sanar ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 27 tare da raunata masu yawa.
Bayanai sun ce maharan sun je kauyen ne da yammaci, inda suka bude wuta su na harbin kan mai uwa da wabi kan mutanen gari, suka kashe masu karar kwana suka raunata masu tsautsayi kamar yadda majiyar ta tabbatar.
Kauyen Kunamawa bai fi nisan kilomita 10 ba daga hedikwatar karamar hukumar Safana ta jihar Katsina. 
Wata majiyar ta ce mutanen da suka rasu, sun kai 30, a yayin da wadanda suka samu raunuka suke kwance a asibiti karkashin kulawar likitoci.
Wasu bayanan sun ce matasan yankin sun gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga don neman agajin hukumomi kan yawaitar hare-haren tun bayan saukar ruwan sama.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu wata sanarwa a hukumance game da harin daga hukumomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara