DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Makiyan jihar Kano ne suka hana gwamnatin Abba ta NNPP yin katabus-Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

-

Makiyan jihar Kano ne suka hana gwamnatin Abba ta NNPP yin wani katabus cikin shekara daya da kama mulki – Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi ‘yan adawa a Kano da karkatar da gwamnati na shekara guda.

Google search engine

Kwankwaso ya bayyana hakanne yayin taron ayyana dokar ta baci kan ilimi a jihar Kano.

Ya ce wannan rana ce mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta baci kan ilimi, domin tun zuwan Abba a matsayin gwamnan yana aiki don za ka ga sawun sa a ko’ina a fadin jihar.

Duk da cewa tun bayan zabe ake fama da zuwa kotu har kusan shekara guda,har zuwa kotun koli,

Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata kotu,kowa ya san cewa Abba ne ya ci zabe.

Amma hakan besa ya kauda kansa wajen hidimtawa al’ummar da suka zabe shi ba kullum aiki yake ba dare ba rana domin wannan shine tsarin mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara