DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojojin Nijar ta hallaka ‘yan ta’adda sama da 100 a sabon farmaki

-

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1wxxPQ8U769PsvIhqS5Hj3jv-T7F1CLG7
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan rana ta Alhamis, rundunar sojojin Nijar din ta sanar da samun nasarar kashe ‘yan ta’adda sama da 100 a yayin wani farmakin ramuwar gayya da ta kai  ta sama da kasa a kan wadanda take zargi da kisan sojojin kasar 20 a yankin Tassia da ke cikin karamar hukumar Téra na jihar Tillaberi a ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata
Kazalika sanarwar rundunar tsaron kasar ta ce daga ranar daya zuwa uku ga watan nan wani samame da ta kai a cikin kasuwannin Dougouro da Bankilare dukkan su cikin karamar hukumar ta Téra ya bata damar hallaka ‘yan ta’adda 8 da kuma kama wasu 19 
A dabra guda kuma rundunar ta ce a ranar daya ga watan dai na Yulin nan da muke ciki ta yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’addar 20 tare da ragargaza kayan aikinsu a yayin wani barin wuta da ta musu a maboyarsu ta sama da ke da nisan kusan kilomita 4 daga arewa da Kokoloko da ke kan iyaka da Burkina Faso

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya...

Mafi Shahara