DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijar, Mali da Burkina Faso ba za su koma kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani na Nijar

-

Nijar, Mali da Burkina Faso ba za su koma kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani na Nijar

Shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya bayyana cewa, al’ummar kasarsa, tare da makwabciyarta Mali da Burkina Faso, sun juya wa kungiyar ECOWAS baya.

Google search engine

Ya bayyana hakan ne a yayin bude taro dake gudana a birnin Yamai tsakanin kasashen yankin Sahel uku da suka fice daga babbar kungiyar a farkon wannan shekarar.

Shugaban hukumar ta ECOWAS, Dr Omar Alieu Touray, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya koka da cewa, duk da kokarin da kungiyar kasashen yankin ke yi na dawo da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, amma kasashen uku ba su nuna wata alamar dawowa ba.

A yayin da yake jawabi a wajen bude taro karo na 92 ​​na majalisar ministocin kungiyar a Abuja, ya ce har yanzu kungiyar ECOWAS ba ta kafa tsarin tattaunawa da mahukuntan kasashen Sahel din uku kan matakin da suka dauka na janye mambobinsu daga kungiyar ba.

A ranar 28 ga watan Junairun da ya gabata ne dai mahukuntan kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara