Rahotanni daga yankin jihar Tillaberi sun tabbatar da tserewar wasu fursunoni da ke tsare a gidan yarin Koutoukalé da ke yankin jihar Tillebari ta Jamhuriyar Nijar.
Bayanan da DCL Hausa ta samu dai na nuni da cewa, gidan yarin na daga cikin gidajen yarin da ke da tsattsauran tsaro kuma mai kunshe da gagga-gaggan ‘yan ta’adda da jagororin su masu hatsarin gaske.
Ma’aikatar cikin gida ta kasar dai tuni ta ce ta ba da umarnin binciko da kuma kamo wadanda suka gudun, don haka ne ma aka ayyana dokar hana zirga-zirga daga bakin karfe 9 na dare a cikin kwaryar birnin Tillaberi.
Gidan yarin Koutoukalé dai da ake kallon sa a mafi tsattsauran tsaro a kasar, dama, an taba dakile wasu hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai masa a shekarar 2016 da 2019.