DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Nijeriya ALGON ta yaba da hukuncin kotun koli na baiwa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai

-

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ta yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.

Shugaban ALGON na kasa Maifata Aminu Mu’azu ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels inda ya yaba da hukuncin wanda yace babban cigaba ne.

Google search engine

A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, Kotun Koli ta umurci Gwamnatin Tarayya ta biya kudaden kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomin.

Ta kuma bayyana matakin da gwamnonin jihohi ke yi na rike kudaden kananan hukumomi a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

A cewar shugaban ALGON, wannan ci gaban ya dace a yi farin ciki dashi, musamman ga wadanda ke karkashin kananan hukumomi. ya ce ya kamata a bar kananan hukumomi su yi abin da ya dace ta hanyar yiwa al’umma aiki,ta haka ne za a gane irin tasirin da ‘yancin yake dashi ga kowace karamar hukuma a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara