DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sudan ta ayyana dokar ta baci, tare da bai bakin haure wa’adin ficewa daga kasar

-

Sudan ta ayyana dokar ta baci, tare da bai bakin haure wa’adin ficewa daga kasar

Gwamnan Khartoum, Ahmed Hamza, ya ba da wa’adin kwanaki 15 ga baki ‘yan kasashen waje su fice daga babban birnin kasar Sudan da kewaye daga ranar Juma’a 12 ga Yuli 2024.

Google search engine

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Sudan da ke Nijeriya ya fitar a karshen makon nan, gwamnan ya ce umarnin da aka ba wa ‘yan kasashen wajen na ficewa daga Sudan an tsara shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Sanarwar ta ce, bisa shawarar kwamitin kula da harkokin tsaro na birnin Khartoum aka bada wannan umurni.

Hukumomin jihar sun baiwa baki wa’adin ficewa daga jihar bisa la’akarin rashin tsaro daya ta azzara a yankin. Jihar Khartoum ta tsawaita wa’adin kwanaki 15 kacal ga baki ‘yan kasashen waje su fice daga jihar, bisa shawarar da kwamitin tsaro ya yanke.

Kwamitin ya gudanar da wani taro don bin diddigin aiwatar da dokar hana fita da babura a yankin kamar yadda sanarwar ta shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na...

APC ta sanar da fara sayar da fom din takarar zaben cike gurbi na majalisar tarayya

Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da...

Mafi Shahara