‘Yan sanda a katsina sun kama wani matashi dake kaiwa ‘yan bindiga bayanai
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 13 da ake zargin yana bayar da bayanai ga ‘yan bindiga.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ya bayyana hakan a Katsina.
A ranar 3 ga watan Yuli, rundunar ‘yan sandan tare da hadin guiwar ‘yan kungiyar sakai a jihar da ke kauyen Dansoda a karamar hukumar Dandume sun yi nasarar cafke matashin mai shekaru 13.
An kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kan munanan ayyukansa. Ya kware wajen bayar da bayanai ga ‘yan bindigar.
A yayin gudanar da bincike, ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, sannan kuma ya ambaci wani Abba, wanda a yanzu haka yake a matsayin wanda ya taimaka masa.
Rundunar ta kuma yi nasarar cafke wani Musaddik Abdullahi da ke zaune a unguwar Kofar Kaura a Katsina, mamban wasu mutane hudu da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.