Bikin zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso na bana ya zo ne daidai lokacin da gwamnan Kano Abba Kabir ke samun shawara daga wasu ‘yan siyasa na cewa ya daina sauraran shawarwarin mai gidan nasa Kwankwaso karkashin kungiyar Abba Ta Tsaya da Kafarka. Amma gwammnan ya yi watsi da wannan shawara inda ya ce a shekaru 38 da ya yi aiki kafada-kafada, da Kwankwaso ya koyi darussan rayuwa da dama, yana mai siffanta madugun siyasar Kwankwasiyyar a matsayin mutum mai gaskiya da jajircewa wajen samar da ci-gaban al’umma.
To amma ba a taru aka zama daya ba, wadanda ke adawa da tsohon ministan tsaron Nijeriyar na masa kallon dan siyasa mai cike da kura-kurai kamar yadda Musa Iliyasu Kwankwaso ke zargi
Masu sharhi kan al’amuran siyasa a Nijeriya irinsu Dr, Sa’idu Ahmad Dukawa na ganin cewa kamata ya yi a wannan lokacin Engr, Rabiu Musa kwankwaso ya mayar da hankali wajen dawo da tarbiyyar matasa musamman yadda maganarsa ke da tasiri a fagen siyasa.
An haifi tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ne a ranar 21 ga Oktoban 1956 a garin Madobi dake jihar Kano, Mahaifin sa Alhaji Musa Sale ya rike mukamin dagacin kauyen Kwankwaso daga bisani aka nada shi hakimin Madobi daga masarautar Kano.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi makarantar firamare a garin Kwankwaso,bayan ya kammala ya wuce Kano Technical College daga nan ya tafi Kaduna Polytechnic inda ya yi karamar Diploma, ya kuma dora da babbar Diploma ta HND.
Tun daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, Kwankwaso, ya kasance shugaban dalibai. Ya yi karatun digirinsa na biyu a Burtaniya daga shekarar 1982 zuwa 1983 a Middlesex Polytechnic da Jami’ar Fasaha ta Loughborough inda ya sami digiri na biyu a fannin injiniya a shekarar 1985. Ya kuma samu shaidar karatun digirin-digirgir na PhD a Jami’ar Sharda da ke kasar India.
Tsohon sanatan na yankin Kano ta Tsakiya ya fara aiki da hukumar samar da ruwan sha ta Jihar Kano a shekarar 1975. Ya yi aiki na tsawon shekaru goma sha bakwai a wurare daban-daban har ya kai matsayin babban injiniyan ruwa.
A shekarar 1992, Kwankwaso ya zama dan majalisar tarayya zuwa shekarar 1993.
Ya zama gwamnan jihar Kano a karo na farko,a shekarar 1999 zuwa 2003. A 2003 bayan shan kayen zaben gwamna da ya yi yunkurin tazarce ya zama ministan tsaron Nijeriya a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo har zuwa 2007.
Sai dai 2011, tsohon gwamnan ya sake fitowa takarar gwamna da karfinsa, inda a tutar jam’iyyar PDP ya samu damar zama gwamnan Kano a karo na biyu har zuwa shekarar 2015.
Daga nan tsohon gwamnan ya zama Sanata a shekarar ta 2015,har zuwa 2019. A shekara ta 2023, Kwankwaso ya yi takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar NNPP. Duk bai yi nasara ba, ya ci gaba da zama jagora ga a cikin jam’iyyarsa ta NNPP wacce a yanzu haka yake fuskantar takaddamar zargin zama maciji fidda na kogo, inda wadansu da suka yi ikirarin kafa jam’iyyar ke zarginsa da mamaye komai a jam’iyyar.
DCL Hausa
Sadeeq Muhammad Fagge daga jihar Kano